Ronaldo na Brazil zai buga wasan bankwana

ronaldo Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ronaldo Nazario de Lima

Gawurtaccen dan kwallon Brazil Ronaldo na shirin yiwa kwallon kafa adabo na dundundun, inda zai buga wasan sada zumunci tsakaninsu da Romania a birnin Sao Paulo wato wasan bankwana.

Hukumar kwallon kafa ta kasar Brazil CBF ta bayyana cewar a ranar bakwai ga watan Yuni za a buga wasan.

A ranar 14 ga watan Fabarairu Ronaldo ya sanarda yin ritaya daga kwallo saboda kiba da kuma rashin koshin lafiya.

Dan shekaru talatin da hudu ya amince ya buga wasan bayan tattaunawarshi da shugaban CBF Ricardo Teixeira.

Teixeira yace "Ronaldo ya cancanci wasan ban kwana, kuma magoya bayanshi nada bukatar kwallonshi a karon karshe sanye da rigar kwallon Brazil".