Dan Mali Sissoko zai yi jinyar watanni uku

sissoko Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mohammed Sissoko na Juventus

Dan kwallon Mali wanda ke taka leda Juventus Mohamed Sissoko zai shafe watanni uku yana jinya saboda rauni a gwiwarshi.

An yiwa dan wasan mai shekaru 26 tiyata a gwiwarshi ta hagu a wani asibiti a Faransa kuma sai a watan Yuni zai koma taka leda.

Abinda hakan ke nufi shine ba zai kara taka leda ba a kakar wasa ta bana da kuma wasannin share fage na Mali a neman gurbin zuwa gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika.

Sissoko yayi ta fama da matsanancin ciwon gwiwa a kakar wasa ta bana.

Juventus zata iya fuskantar matsaloli saboda jinyar tashi saboda a halin yanzu itace ta bakwai akan tebur na gasar serie A sannan zata buga babban wasa tsakaninta da AC Milan a ranar Asabar.