Kocin Togo Thierry Froger ya yi murabus

togo
Image caption Wasu daga cikin 'yan kwallon Togo

Kocin tawagar 'yan kwallon Togo Thierry Froger ya ajiye mukaminshi ba tare da jinkiri ba,inda ya koma kungiyar Nimes ta Faransa.

A ranar Talata ne kocin ya baiwa hukumar kwallon Togo takardarshi ta murabus, in ji kakakin hukumar Komlan Ekpe.

Ekpe yace"Froger ya bukaci hukumar ta barshi ya tafi , bisa wasu dalilai na kashin kanshi, kuma ya ce baya bukatar a bashi wasu kudade".

Froger ya maye gurbin Hubert Velud a watan Yunin bara inda ya kulla yarjejeniyar watanni 18.

A wasanni taran daya jagoranci Togo, babu wasan data samu nasara ko guda.

Togo a yanzu itace ta hudu a rukunin K na neman gurbi a gasar cin kofin kasashen Afrika na 2012.

Cikin kasashe biyar din dake rukunin, biyu ne kadai zasu tsallake zuwa gasar a Equatorial Guinea da Gabon a badi.