An nada Norman Mapeza a matsayin kocin Zimbabwe

norman Hakkin mallakar hoto b
Image caption Norman Mapeza

An nada tsohon dan kwallon baya na Zimbabwe Norman Mapeza a matsayin sabon kocin mai horadda 'yan kwallon kasar.

Kwangilar Mapeza zata kaishi har zuwa lokacin gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika a shekara ta 2012, sannan ya maye gurbin Sunday Chidzambwa.

Mapeza tsohon dan kwallon kungiyar Galatasaray na Turkiya, shine kocin riko na kasar inda suka fara kampe na neman gurbi a gasar cin kofin Afrika da kafar dama inda suka tashi kunen doki tsakaninsu da Liberia.

A baya lokacin da kwangilar Tom Saintfeit na Belgium ya Zimbabwe, Mapeza da Madinda Ndlovu ne suka jagoranci tawagar 'yan kwallon kasar.

Mapeza tsohon kocin Warriors ne sannan kuma shine dan kasar Zimbabwe na farko daya buga gasar cin kofin zakarun Turai tare da Galatasaray.