2014:Fifa zata yi amfani da na'urar fasaha a raga

goal Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kwallon Frank Lampard da aka hana

Shugaban Fifa Sepp Blatter ya ce za ayi amfani da na'urar fasaha a raga lokacin gasar cin kofin duniya na shekara ta 2014 a Brazil, idan har an samu tsarin da dace a lokacin.

Za a cigaba da gudanar gwaje gwaje don duba tsarin daya fi dacewa daga nan zuwa shekara mai zuwa kamar yadda hukumar dake kafa dokokin kwallon kafa wato Ifab ta gindaya.

Blatter a jawabinshi lokacin taron Ifab a Wales ya ce:"Idan har ya yi aiki to babu matsala a 2014".

Blatter ya canza ra'ayin aka amfani da na'urar fasaha a ragar kwallo bayanda akan ki amince da kwallon da Frank Lampard ya zira a wasansu da Jamus a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.

Da aka sake duba bugun da Lampard yayi, sai aka gano cewar kwallon ta shiga ragar, amma alkalin wasa da mataimakanshi duk basu shigar kwallon ba.

Daga karshe Jamus ce ta samu nasara akan Ingila daci hudu da daya.