Liverpool ta casa Manchester United daci uku da daya

kuyt
Image caption Dirk Kuyt ya bar Van der Saar a kwance

Dirk Kuyt ya ci kwallaye uku shi kadai inda ya kara fadada takarar gasar premier ta Ingila a wasan da Liverpool ta casa Manchester United a Anfield daci uku da daya.

Sir Alex Ferguson ya fara murna ganin cewar Arsenal ta tashi canjaras tsakaninta da Sunderland, amma sai United ta kasa amfani da damar don kara tazara tsakaninta da gunners.

Kuma wannan ne rashin nasara biyu a jere da United ta fuskanta bayan da Chelsea ta bata kashi, a yanzu kenan United ta dara Arsenal da maki uku duk da cewar Arsenal nada kwantan wasa.

Sakamakon sauran wasannin gasar premier:

*Birmingham City 1 - 3 West Bromwich *Arsenal 0 - 0 Sunderland *Bolton Wanderers 3 - 2 Aston Villa *Fulham 3 - 2 Blackburn Rovers *Newcastle United 1 - 2 Everton *West Ham United 3 - 0 Stoke City *Manchester City 1 - 0 Wigan Athletic