UEFA:Wilshere zai buga,Puyol ya samu rauni

wilshere
Image caption Matashin dan kwallon Arsenal Jack Wilshere

Dan kwallon Arsenal Jack Wilshere yace lafiyarshi kalau zai iya buga wasansu da Barcelona na gasar zakarun Turai a ranar Talata.

Dan wasan tsakiyan ya murmure daga rauni a idon sawunshi a wasanda suka tashi canjaras tsakaninsu da Sunderland abinda ya hanashi shiga horo a ranar Lahadi.

Theo Walcott da Robin van Persie duk ba zasu buga wasan ba, amma kuma kaptin Cesc Fabregas da Alex Song ana tababbar lafiyarsu.

An bangaren Barcelona kuwa kaptinta Carles Puyol ba zai buga ba saboda rauni a gwiwarshi.

Rashin shi yasa Barca zata yi rashin manyan wasanta na baya saboda an dakatar da Gerard Pique.

A halin yanzu dai zabin da mai horadda 'yan Barca Pep Guardiola ke dashi shine cikin wadanan kwallo ukun: Eric Abidal, Gabriel Milito da Sergi Busquets.

A bugun farko a filin Emirates, Arsenal ta samu galaba akan Barcelona daci biyu da daya.