Da kamar wuya mu lashe gasar Premier- Ancelotti

Image caption Carlo Ancelotti

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce da wuya kungiyar ta lashe gasar Premier ta bana, duk da nasarar da kungiyar ta samu a kan Blackpool a gasar.

Chelsea dai ta bi Blackpool har gidanta inda ta cassa ta da ci uku da guda.

A yanzu haka dai maki tara ne ke tsakanin Chelsea da Manchester United wadda ke jan ragama a gasar ta Premier, sannan kuma Chelsea na da kwanten wasa guda.

"Mu dai burin mu shine mu kammala kakar gasar ta bana cikin rukunin kungiyoyi hudu dake kan tebur a gasar." In ji Ancelotti

"Muna kusa da Manchester amma burin mu shine mu lashe duk wani wasa da zamu buga a nan gaba, kuma idan muna da rabo, shi kenan".