An kauracewa filayen wasa a Angola bayan kamalla gasa

angola Hakkin mallakar hoto b
Image caption Filin wasa na Luanda

Watanni goma sha uku kenan da Angola ta dauki bakuncin gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika.

Amma dai filayen wasa hudun da aka gina musamman don gasar, sunanan ba'a amfani dasu kuma babu wanda yasan makomarsu.

Filayen wasan sune a Luanda da Lubango da Benguela da Cabinda, kuma an rufe su a yayinda aka katse wutar lantarkinsu.

A makon daya gabata ne wakilin BBC ya ziyarci katafaren filin wasa na Luanda mai cin 'yan kallo 50,000, inda ya gani an kauracewa wajen.

A halin yanzu ciyawa ta mamaye babbar mashigar filin wasan da kuma inda ake ajiye motoci.

Tun watan Junairun 2010, ba kasafai ake amfani da filayen wasan ba, amma dai a watan Nuwamban bara an gudanar da bukin zagoyowar ranar 'yancin kai na Angola a Luanda.

Kungiyoyin kwallon kafa na kasar sun ki hayar filayen wasan saboda a cewarsu yayi tsada dayawa.

Rahotanni sunce ana bada hayar filayen wasan akan dala dubu ashirin da biyar akan kowanne wasa, kudin da kungiyoyin kwallon kafa a Angola ba zasu iya biya ba.