Watakila Fabregas ya buga wasanmu da Barca

Cesc Fabregas
Image caption Cesc Fabregas

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce Cesc Fabregas watakila ya buga wasansu da Barcelona na zagaye na biyu a gasar zakarun Turai.

Arsenal dai zata buga wasan ba tare da wasu manyan 'yan wasanta ba a Nou camp, a yayinda Gunners din ke kokarin kare nasarar ci biyu da daya a bugun farko.

Amma dai akan batun Kaptin dinshi wanda bai buga wasanni uku a jere ba, Wenger ya ce "ya murmure da kashi casa'in cikin dari."

Sai dai Jack Wilshere ya ce lafiyarshi kalau zai iya buga wasan amma dai Alex Song ba zai buga ba saboda rauni a gwiwa, kamar yadda Theo Walcott da kuma Robin van Persie duk ba zasu buga ba.

A bangaren Barcelona kuwa raunin zai hana Carles Puyol bugawa a yayinda aka dakatar da Gerard Pique.

Haka zalika kocin Barcelona Pep Guardiola yana fama da ciwon baya, amma anasaran zai kasance da 'yan wasanshi a Nou Camp.