Van der Vaart da Bale zasu murmure kafin wasanmu da Milan

bale
Image caption Van der Vaart da Gareth Bale ne zakarun Spurs

Kocin Tottenham Harry Redknapp na fatar 'yan kwallonshi Rafael van der Vaart da Gareth Bale zasu murmure kafin wasansu da AC Milan na zagaye na biyu na gasar zakarun Turai.

Van der Vaart na fama da rauni a kafarshi a yayinda Bale ya shafe makwanni shida yana jinyar ciwon baya.

Redknapp ya ce"zamu kai harin cin kwallo ne kawai, don Lennon da Bale zasu shiga gaban".

Tun watan Fabarairu rabon da Van der Vaart ya takawa Spurs leda.

A yayinda shi kuma Bale ya buga wasanshi na farko a ranar Lahadi tun bayan daya raunata a watan Junairu.

A bugun farko tsakanin Spurs da Ac Milan a filin San siro dai, Spurs din ce ta samu galaba daci daya me ban haushi.