2012:Afrika ta Kudu zata kara da Masar a Ellis Park

afrika
Image caption 'Yan Afrika ta Kudu a filin wasa

Afrika ta Kudu ta maida wasanta da Masar na neman gurbin zuwa gasar cin kofin Afrika zuwa filin Ellis Park dake Johannesburg

A baya Bafana Bafana zata kara da Pharaohs ne a filin wasa na Soccer City.

Amma kuma akwai damuwa akan ingancin filin wasan na Soccer City inda aka buga wasan karshe na gasar cin kofin duniya a bara, shi yasa akan canza.

Shugaban hukumar kwallon Afrika ta Kudu-Safa Kirsten Nematandani ya tabbatarwa BBC sauyin da aka samu.

Nematandani yace" za a buga wasan ne a Ellis Park".

A halin yanzu dai Masar ce ta karshe a rukunin G inda take da maki guda daga wasanni biyun data buga.