Jermain Defoe na tunanin barin Tottenham

defoe Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jermain Defoe

Dan wasan Tottenham Jermain Defoe ya ce yayi tunanin canza sheka a watan Junairun data wuce saboda rashin sashi wasa.

Dan kwallon mai shekaru 28 wanda ya shafe shekaru shida a Spurs, a kakar wasa ta bana wasanni 11 aka fara tare dashi a yayinda aka shigo dashi bayan hutun rabin lokaci sai uku.

Defoe ya shaidawa Daily Mail cewar "wani lokaci sai inyi tunanin me nake yi, ina cin benci, gwamma in tafi".

Defoe a baya ya taba barin Spurs ya koma Portsmouth a shekara ta 2008 da 2009.

Amma dai tsohon dan kwallon West Ham din ya ce baya tunanin za a hanashin barin White Hart Lane koda a matsayin aro ne.