Kaka zai yi jinya ta makwanni biyu saboda turgude gwiwa

kaka
Image caption Kaka

Dan Brazil wanda ke taka leda a Real Madrid Kaka zai shafe karin makwanni biyu yana jinya saboda turgude gwiwarshi ta hagu.

Sanarwar da Real Madrid ta fitar ta ce Kaka na bukatar kulawa don yana cikin damuwa matuka akan gwiwarshi ta hagu.

Dan shekarau 28, Kaka an yi mashi tiyata a watan Agusta inda ya komo horo a watan Disamba.

Real ta ce dan wasan zai shafe kwanaki goma sha biyar ana duba lafiyarshi tare da yi mashi gashin kashi.

Wannan raunin yana nufin cewar Kaka ba zai buga wasan Real da Lyon na gasar zakarun Turai a mako mai zuwa.

A farkon wannan watanne kocin Real Jose Mourinho ya ce baya matsawa tsohon dan kwallon AC Milan din ya koma taka leda yadda ya saba.