FIFA: Ghana na jan ragamar sauran kasashen Afrika

fifa
Image caption FIFA

A bisa jerin da hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta fitar akan yadda karfin kasashe yake a fannin kwallon kafa a duniya a watan Maris, har yanzu Ghana ce ta farko a Afrika amma ta goma sha shida a duniya. Sai Ivory Coast wacce ta zama ta biyu a gaban Masar, a yayinda Najeriya ke ta hudu a duniya amma ta talatin da tara a duniya. Jerin kasashe goma na farko a Afrika:

1. Ghana (16 a duniya) 2. Ivory Coast (25 a duniya) 3. Masar (35 a duniya) 4. Najeriya (39 a duniya) 5. Burkina Faso (40 a duniya) 6. Kamaru (42 a duniya) 7. Guinea (44 a duniya) 8. Tunisia (45 a duniya) 9. Afrika ta Kudu(46 a duniya) 10.Algeria (55 a duniya)

Sai a duniya baki daya Spain ce ke cigaba da jan ragama a yayinga Netherlands ke ta biyu.

1. Spain 2. Netherland 3. Jamus 4. Argentina 5. Brazil