'Mun yi ba zata a gasar zakarun Turai'- Redknapp

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Harry Redknapp

Kocin Tottenham Harry Redknapp ya ce kungiyar shi tayi matukar bazata da ta tsallake zuwa matakin wasan dab da kusa dana karshe a gasar zakarun Turai.

Spurs dai ta buga canjarasa a wasan da ta buga da AC Milan a filin Whitehart lane bugu na biyu.

A bugun farko Spurs ta doke AC Milan da ci daya mai ban haushi a filin San Siro.

"Wannan wani babban abun ne da mu ke ganin ba zai yiwuwa, sai kuma gashi mun samu nasara," In ji Redknapp.

"Shekaru biyu da suka wuce, idan wani ya ce mun zamu kai wasan zagayen dab da kusa dana karshe a gasar zakarun Turai, zan dauka bashi da hankali ne."