Kocin Black Stars Stevanovic ya gayyaci Tagoe

tagoe Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Prince Tagoe

Kocin Black Stars Goran Stevanovic ya tabbatarwa da dan wasan Ghana Prince Tagoe cewar zai dinga sashi a wasa.

Dan shekaru 24 ya zira kwallaye uku a wasanninshi biyu na farko a Partizan Belgrade.

Tagoe ya koma Partizan a matsayin aro daga Hoffenheim a watan daya gabata, kuma ya bugawa Ghana a gasar cin kofin duniya a bara.

Saboda an dakatar da Asamoah Gyan a wasan Ghana na gaba, Stevanovic na son amfani da Tagoe a gaba.

Stevanovic yace"Tagoe na kan ganiyarshi, a don haka muna bukatarshi a wasanmu da Congo a ranar 27 ga wannan watan".

Tagoe ya ci kwallaye biyar a wasanni 25 daya bugawa Ghana.

A halin yanzu dai Ghana ce ke jan ragamar rukunin da take da maki hudu cikin karawa biyu.