Wenger ya musanta zargin da Uefa tayi mashi

wenger Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Wenger da Busacca

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya musanta zargin da Uefa tayi mashi na saba ka'ida a kalamanshi ga alkalin wasa Massimo Busacca bayan an fiddasu a gasar zakarun Turai.

Ana tuhumar Wenger akan yin amfani da kalaman da basu dace ba akan alkalin wasan dan kasar Switzerland, inda Barcelona ta casa Arsenal daci uku da daya a ranar Talata.

A wasan dai an kori dan Arsenal Robin van Persie a wani yanayi mai cike da kace nace.

Wenger yace"ban amince da tuhumar ba, ban gane daga ina ya fito ba, abin kunya ne da alkalin wasan ya kori van Persie".

A cewar Wenger "kamata yayi Uefa ta nuna tawali'u ta kuma nemi afuwar abinda ya faru, ba wai ta tuhumi wadanda basu da laifi".