Gerrard zai yi jinyar makwanni hudu

Gerrard
Image caption Steven Gerrard ya dade yana fama da rauni

An yiwa kyaftin din Liverpool Steven Gerrard tiyata, wacce ta tilas ta masa yinjar makwanni hudu ba tare da taka leda ba.

"An dauki matakin ne bayan tattaunawa da likitoci," a cewar sanarwar da kulob din ya fitar.

Dan wasan na Ingila ba ya cikin tawagar Liverpool da ta yi tattaki zuwa Braga domin fafatawa a gasar cin kofin Europa.

Idan ya shafe wata guda yana jinya, Gerrard ba zai taka leda a wasan da Ingila za ta kara da Wales ba a gasar share fagen shiga gasar kasashen Turai na 2012.

Gerrard ya samu raunin ne a wasan da Liverpool ta samu nasara da ci daya da nema a kan Chelsea a ranar 6 ga watan Fabreru a filin wasa na Stamford Bridge.