Kofin FA:Manchester United zata fafata da Manchester City

ferguson
Image caption Ferguson da Mancini

Manchester United zata kara da babbar abokiyar hammayarta Manchester City a wasan kusada karshe na gasar cin kofin FA na Ingila.

City din ta doke Reading a wasan zagayen gabda na kusada karshe daci daya me ban haushi.

Bolton wacce ta lallasa Birmingham zata hadu ne da Stoke City wacce ita kuma ta casa West Ham.

Yadda zubin yake:

*Manchester City ko Reading v Manchester United *Bolton Wanderers v Stoke City

A ranakun 16 da 17 na watan Afrilu ne za a buga wasan a filin Wembley.