Dan Ivory Coast Fae zai yi jinya ta watanni uku

fae Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Emerse Fae

Dan kwallon Ivory Coast wanda ke taka leda a Nice Emerse Fae ba zai kara taka leda ba a kakar wasa ta bana saboda rauni a cinyarshi.

Abinda hakan ke nufi shine dan wasan mai shekaru 27 ba zai bugawa kasarshi wasanta na share fagen buga gasar cin kofin Afrika ba.

Likitoci ne suka gano tsananin ciwon bayan sun gudanar da gwaje gwaje.

Kocin Nice Eric Roy yace"mun samu sakamakon gwajin, kuma baida kyau".

A halin yanzu dai Ivory Coast ce ta farko a rukunin da take, kuma a karshen wata zata fafata da Benin a Abidjan.

Ana saran Fae zai komo taka leda a watan Yuni.