An fidda Arsenal a gasa uku cikin makwanni biyu

wenger Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wenger da Ferguson

Kocin Arsenal Arsene Wenger na kokarin gano bakin zaren sakamakon fidda kulob din daga manyan gasanni uku a cikin makwanni biyu.

Gunners sun sha kashi daci biyu da nema a hannun Manchester United a gasar cin kofin FA, bayan da aka fidda Arsenal din a gasar zakarun Turai da kuma na cin kofin Carling.

Wenger ya ce "muna da babban kalubale a gabanmu, tunda a yanzu gasar premier kadai ta rage mana".

Arsenal na kokarin lashe kofin farko tun kofin FA na shekara ta 2005 data lashe.

A halin yanzu Arsenal ce ta biyu akan teburin gasar premier ta Ingila, inda United ta dara ta da maki uku.

Kuma Wenger ya ce da zarar United tayi kuskure, tabbas zasu yi amfani da wannan damar don lashe gasar. Ita kuwa United a halin yanzu tana kokarin lashe kofin uku ne, wato na premier dana FA da kuma na zakarun Turai.