Rashin kyawun filaye ne yasa 'yan kwallo ke gudun Serie A

Beckenbauer
Image caption Franz Beckenbauer

Tsohon gawurtaccen dan kwallon Jamus Franz Beckenbauer ya ce rashin kyawun filayen wasa a Italiya ne hujjar data sanya yawancin 'yan kwallo ba sa son bugawa a gasar Serie A.

A cewar bajamushen, shirya gasa ta kasa da kasa a kasar ne kawai zata janyo 'yan kwallo su koma buga a gasar.

Beckenbauer yace"a baya,kowa nason ya buga a Serie A,amma a halin yanzu ba haka lamarin yake".

Ya kara da cewar"ina tunanin cewar filayen kwallo sun taka muhimmiyar rawa wajen dakushewar kwallon kafa a Italiya".

Akan wasan Bayern Munich da Inter Milan kuwa Beckenbauer ya ce yana ganin cewar Inter tafi karfi.