FIFA:Bin Hammam zai bayyana matsayinshi a ranar Juma'a

blatter Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sepp Blatter da Bin Hammam

Ana saran a ranar Juma'a Mohamed Bin Hammam zai bayyana ko zai yi takara da Sepp Blatter a shugabancin Fifa na watan Yuni.

Hukumar dake kula da kwallon nahiyar Asiya ta ce shugabanta wanda dan kasar Qatar ne zai fayyace matsayinshi akan batun zaben.

Blatter na neman wa'adi na hudu a shugabancin Fifa.

Koda yake kawo yanzu babu wanda ke hammaya da Blatter amma dai Bin Hammam ya nuna alamun cewar zai kalubalen ceshi a takara Fifa din.

A makon daya gabata ne aka rantsar da Bin Hammam babu hammaya akan shugaban kwallon Asiya a karo na uku, sannan ya ce yanada goyon bayan nahiyoyi biyar ko shida, amma babu tabbas ko nahiyar Turai zata goyi bayanshi.

A ranar 31 ga watan Maris ne za'a rufe bayyana nuna aniyar takarar shugaban Fifa.