Coventry City ta kori kocin 'yan kwallonta Boothroyd

Aidy Boothroyd Hakkin mallakar hoto b
Image caption Aidy Boothroyd

Kungiyar Coventry City ta Ingila ta sallami kocin 'yan kwallonta Aidy Boothroyd sakamakon samun nasara a wasa guda cikin karawa 16.

Boothroyd mai shekaru 40 a watan Mayun bara ne aka nadashi kocin Coventry bayan tafiyar Chris Coleman.

Mataimakinshi Martin Pert shima ya barsu da daya kocin Steve Harrison a yayinda aka nada Andy Thorn a matsayin kocin riko.

Coventry a halin yanzu itace ta goma akan tebur, kuma ta nada masu horadda 'yan kwallo goma cikin shekaru goman da suka wuce.

Boothroyd ya bar Colchester United bayan shafe shekaru tara da rabi don komawa Ricoh Arena.

A baya ya jagoranci Watford inda ya jagoranceta zuwa gasar premier a shekara ta 2006.