Joachim Loew zai cigaba a Jamus har zuwa 2014

loew
Image caption Joachim Loew

Joachim Loew ya sabunta yarjejeniyarshi da Jamus don cigaba da jan ragamar tawagar 'yan kwallon kasar har zuwa gasar cin kofin duniya na 2014.

A ranar Talata ne hukumar kwallon Jamus ta sanarda cewa dan shekaru hamsin da dayan ya rattaba hannu a kwangilar.

A shekara ta 2006 ne aka nada Loew a matsayin kocin Jamus inda ya maye gurbin Juergen Klinsmann.

Abinda hakan ke nufi shine Loew tare da mataimakinshi Hansi Flick da Andreas Koepke da Oliver Bierhoof zai jagoranci Jamus zuwa Brazil a shekara ta 2014.

Loew ya haskaka matuka a matsayinshi na kocin Jamus inda ya samu nasara akan wasanni 43 cikin karawa 63 inda ya buga canjaras a fafatawa 11, har wa yau Jamus ta sha kashi wasanni tara cikin shekaru hudu da rabin da aka baiwa Loew.

Sabunta wannan yarjejeniyar ya kawo karshen batun alakanta Joachim Loew da Bayern Munich.