Ba a gayyaci Mokoena a tawagar Bafana Bafana ba

mokoena
Image caption Aaron Mokoena

Kocin Afrika ta Kudu Pitso Mosimane bai gayyaci kaptin dinsa Aaron Mokoena ba cikin tawagar 'yan kwallon da zasu kara da Masar a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin Afrika na badi.

Dan kwallon Portsmouth din ya kasance dan Afrika ta Kudu na farko da ya taka mata leda a wasanni 100 kafin gasar cin kofin duniya na bara.

Amma saboda Mokoena bai bugawa, shi ya sanya Mosimane yaki gayyatarshi.

Mosimane yace"muna bukatar tawagar 'yan kwallon gogaggu saboda wannan babban wasan".

A watan daya gabata, Mokoena ya zauna a benci a wasan Afrika ta Kudu da Kenya.