Capello na tunanin mayarwa Terry mukamin kaptin

terry
Image caption John Terry

Kocin Ingila Fabio Capello na tunanin karbar kambum kaptin wajen Rio Ferdinand don mayarwa John Terry.

Ferdinand na fama da rauni abinda zai hanashi buga wasan Ingila da Wales a ranar 26 ga watan Maris.

A bara ne aka karbe kambum kaptin daga wajen Terry, amma Capello na son ya gujewa abinda ya faru a wasan sada zumunci da Denmark inda aka yita karba karba da kambum.

Capello yace"ina ganin ladabtarwa ta shekara guda tayi haka, wannan ne lokacin da yafi dacewa John Terry ya sake shugabanci, kuma a mataki na dun dun dun".

Ganin cewar mataimakin kaptin Steven Gerrard ba zai buga wasan ba saboda rauni, ana saran Capello zai bayyana matsayinshi kafin wasan da za ayi a filin Millennium.

A cewarshi haka zai sa a kaucewa abinda ya faru a Copenhagen a watan daya gabata inda Frank Lampard ya rataya kambum, sannan ya baiwa Gareth Barry daga karshe kuma Ashley Cole ya saka.