Za a koma gasar kwallon Masar a watan Afrilu

ahly Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Magoya bayan Al Ahly

Za a koma gasar kwallon Masar a ranar 15 ga watan Afrilu bayan dakatarwa ta watanni uku, sakamakon zanga zangar data kawar da shugaba Hosni Mubarak.

Hukumar dake kula da kwallon Masar ta ce gasar wacce aka fara a watan Agustan bara, za a kamalla a ranar 10 ga watan Yuli.

An dakatar da gasar ce a watan Junairu saboda zanga zangar kin jinin gwamnati a Alkahira da wasu biranen kasar.

Wannan labarin zai yiwa kulob kulob dadi, ganin cewar kudaden shigar ya kafe saboda an daina taka leda.

Kafin a dakatar da gasar, Zamalek ce ke jan ragama da maki 32 inda take kokarin lashe kofinta na farko tun shekara ta 2004, a yayinda Ismaily ke ta biyu da maki 29.

Babbar abokiyar hammayar Zamalek din wato Al Alhy ce ta hudu da maki 26.