An dakatar da Ferguson na wasanni biyar

fergie Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Sir Alex Ferguson na korafi

Kotun dake kula da hukumar kwallon Ingila ta dakatar da Sir Alex Ferguson na wasanni biyar saboda kalamanshi akan alkalin wasa Martin Atkinson.

An kama kocin Manchester United da laifin aikata ba dai dai ba wajen sukar Atkinson bayan da Chelsea ta doke su a watan daya gabata.

Ferguson ya shaidawa MUTV cewar"munason alkalin wasa mai adalci,amma bamu samu haka ba".

Dakatarwar zata fara aiki ne daga ranar 22 ga watan Maris, ta hada da wasan FA tsakanin United da Manchester City.

Har wa yau kotun taci tarar Ferguson pan dubu talatin.

Bayan sa'o'i ashirin da hudu za a aikewa da Ferguson sakon laifinshi, sannan bayan sa'o'i 48 yana damar daukaka kara.

Idan har ya amince da laifin, to Ferguson mai shekaru 69 ba zai shiga cikin fili ba a wasansu da West Ham, Fulham, Everton da kuma Arsenal sai kuma na kofin FA da City a filin Wembley.