Ferguson ya jinjinawa Hernandez akan kwazo

hernandez
Image caption Javier Hernandez

Sir Alex Ferguson ya ce da mamaki yadda Javier Hernandez ya gano dabarun kwallo cikin kankanin lokaci bayan da matashin ya taimakawa Manchester United ta fidda Marseille a ranar Talata.

Dan kasar Mexico mai shekaru 22, ya koma Old Trafford ne daga kungiyar Chivas de Guadalajara, inda yaci kwallaye biyu a wasan zakarun Turai.

Ferguson yace"abin mamaki, mun dauka zai shafe lokaci mai tsawo kafin ya gano bakin zaren".

Hernandez yaciwa United kwallon farko 'yan mintuna da fara wasa bayanda Wayne Rooney ya bashi kwallo, sannan a minti na 75 Ryan Giggs ya bashi kwallon na biyu.

Marseille daga bisani ta farke kwallo daya bayanda Wes Brown yaci kansu, amma duk da haka United ta tsallake zuwa zagayen gabda na kusada karshe.

Hernandez ya zira kwallaye 16 cikin wasanni 33 daya bugawa United.