Lehmann zai kasance tare damu zuwa Mayu-Wenger

lehmann Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jens Lehmann

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya tabbatar da cewa Jens Lehmann ya fara horo tare da kulob din inda zai kulla yarjejeniya har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Dan shekaru arba'in da daya, tsohon golan Jamus din baida kungiya tun bayan da yayi ritaya a bara, bayan ya shafe shekaru biyu a Stuttgart.

Raunin Wojciech Szczesny da Lukasz Fabianski da kuma Vito Mannone, ya janyo Arsenal nada lafiyayen gola daya ne wato Manuel Almunia.

Lehmann ya kamawa Arsenal a wasanni 199 daga shekara ta 2003 zuwa 2008.

Arsene Wenger yace: "Lehmann na horo tare damu, kuma zai sanya hannu a kwangila zuwa karshen kakar wasa ta bana".

Lehmann ya lashe gasar Premier da Arsenal a shekara ta 2003/2004 kuma ya kasance babban dan wasan kulob din a wancan lokacin.

Ya bugawa Jamus a karawa 61 kafin ya bar Arsenal a shekara ta 2008 lokacin da Manuel Almunia ya shiga gabanshi.