Ina nan daram a United, babu inda zan je-Rooney

rooney
Image caption Sir Alex Ferguson da Wayne Rooney

Dan wasan Manchester United Wayne Rooney ya musanta rahotannin dake cewar zai bar Old Trafford.

Dan kwallon mai shekaru ashirin da biyar, ya kara kula wata sabuwar kwangila ta shekaru biyar da United a watan Oktoban bara, kuma ya ce zai cigaba da taka leda a kulob din har zuwa yakai shekara talatin a duniya.

Rooney yace"naga rahotanni, ban taba gannin shirma irinsa ba a rayuwata, kuma bani da wata matsala da Sir Alex Ferguson".

Ya kara da cewar:"idan bana jin dadin wasana ana, ai bazan sabunta kwangila ta ba".

Har wa yau Rooney ya yi murnar baiwa Javier Hernandez kwallo a wasan da United ta fidda Marsielle a gasar zakarun Turai.

Koda yake dai , dan wasan yayi fama da ciwo a idon sawunshi, amma a cewarshi a yanzu baida watan matsala.