Zakarun Turai: Chelsea za ta kara da Man U

UEFA
Image caption Za a buga wasannin ne a ranakun 5 da 6 da kuma 12 da 13 na watan Afrilu

Chelsea za ta kara da Manchester United a zagayen gab da na kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai.

Wannan karawa dai maimaici ce ta wasan karshe na gasar da kungiyoyin biyu suka buga a shekara ta 2008, inda United ta samu nasara.

Mai rike da kanbun Inter Milan za ta fafata da Schalke 04 na kasar Jamus.

Sai Barcelona da za ta kara da Shakhtar Donetsk na kasar Ukraine.

Real Madrid za ta kece raini ne da Tottenham na Ingila, wacce ta fitar da AC Milan na Italiya.

Duk wanda ya yi nasara tsakanin Chelsea da Manchester United, zai kara da wanda ya yi nasara tsakanin Inter Milan da Schalke 04.

Yayin da wanda ya samu nasara tsakanin Barcelona da Shakhtar Donetsk, zai fafata da wanda ya yi nasara tsakanin Real Madrid da Tottenham.

Za a buga wasannin ne a ranakun 5 da 6 da kuma 12 da 13 na watan Afrilu.