A watan Mayu Ancelotti zai san makomarshi a Chelsea

ancelotti
Image caption Carlo Ancelotti

Shugaban Chelsea Ron Gourlay ya ce sai bayan karshen kakar wasa ta bana, za a tattance makomar kocin kulob din Carlo Ancelotti.

Ancelotti ya lashe kofina biyu a kakar wasa ta farko daya jagoranci Chelsea, amma a yanzu har an fidda kulob din daga gasa biyu a Ingila.

Gourlay ya shaidawa BBC cewar "zamu yanke hukunci akanshi a watan Mayu, kuma kwangilarshi za ta kare ne a shekara ya 2012.

Ya kara da cewar Carlo babban koci ne a duniya saboda ya taba lashe gasar zakarun Turai a matsayin koci da kuma matsayin dan wasa.

Sakamakon korar Ray Wilkins a watan Nuwamban bara, Chelsea ta samu maki shida ne kacal cikin wasanni bakwai, abinda ya sanya a yanzu ba zata takarar lashe gasar premier.