Najeriya ta gayyaci dan kwallo Wigan Victor Moses

moses
Image caption Victor Moses na Wigan da Aurellio na Liverpool

Najeriya ta gayyaci dan kwallon Wigan Victor Moses cikin tawagar Super Eagles da zasu fuskanci Ethiopia a wasan share fage na neman gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika a badi.

Mataimakin kocin Super Eagles Simon Kalika ya bayyana cewar"mun kira Moses saboda mun gudanar da sauye- sauye a tawagar da zata kara da Ethiopia a karshen mako".

Wakilin Moses, Tony Finnigan ya bayyana cewar dan kwallon Wigan din zai hade tare da sauran 'yan wasan Najeriya da kuma Victor Obinna a ranar Litinin.

A wasan sada zumuncin da Najeriya ta kara da Sierra Leone a watan daya gabata, an gayyaci Victor Moses amma kuma bai amsa gayyatar ba.

Moses mai shekaru 20, a baya ya bugawa Ingila kwallo a matakin 'yan kasada shekaru 17 da 19 da kuma 21.