Uefa: Ba zamu rage farashin tikitin wasan karshe ba

platini
Image caption Michel Platini

Hukumar dake kula da kwallon Turai Uefa ta ce ba zata rage farashin tikitin shiga kallon wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai da za ayi a Wembley.

Shugaban Uefa Michel Platini ya ce "ba zamu rage farashin ba, amma za mu duba lamarin a nan gaba".

'Yan kallo zasu biya pan 176 a matsayin kudi mafi karanci, amma kuma magoya bayan kulob din da zasu buga wasan karshen zasu biya pan tamanin don su cire kwarkwatar ido.

Za a buga wasan karshen ne a filin Wembley mai cin 'yan kallo dubu 86 a ranar Asabar 28 ga watan Mayu.

Tuni dai aka fara sayarda tikitin shiga fili don kallon wasan idan ranar ta yi.

Wannan ne zai zamo karo na biyu da za a buga wasan karshen a ranar Asabar, sabannin tsakiyar mako da aka sabayi, abinda Platini ya ce zai baiwa iyalai damar zuwa kallon wasan.

Hukumar dake kula da kwallon Turai-Uefa a baya ta bayyana cewar farashin tikitin an kwatatanshi ne da manyan wasanni kamar na wasan karshe na gasar cin kofin kwallon duniya.