Zan sauka daga shugabancin Fifa a 2015-Blatter

fifa Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sepp Blatter da Bin Hammam na kalubalantar juna

Sepp Blatter ya ce zai sauka daga kujerar shugabancin Fifa a shekara ta 2015, idan har aka sake zabenshi a karo na hudu a watan Yuni.

Dan shekaru 75, wanda yake shugabancin hukumar kwallon duniya tun shekarar 1998, yana fuskantar kalubale ne daga wajen shugaban hukumar kwallon nahiyar Asiya Mohammed Bin Hammam.

Blatter ya shaidawa taron Uefa a ranar Talata cewar"kun san ina neman wa'adin karin shekaru hudu, amma wannan ne zai zamo shekarar karshe da zan tsaya takara".

Za a gudanar da zaben sabon shugaba a taron kolin Fifa da za a fara a ranar 31 ga watan Mayu.

A yayinda Bin Hammam ya sha alwashin kara yadda ake daukar hukunci a Fifa, Blatter na fuskantar kalubale na farko tun bayan da Issa Hayatou yayi takara dashi a shekara ta 2002.

Bin Hammam shima a halin yanzu yana halartar taron kolin hukumar kwallon Turai wato Uefa, saboda duk su biyun na kamun kafa wajen wakilan kasashe kafin zaben na Fifa a Zurich a ranar daya ga watan Yuni.