An sake zaben Platini a Uefa babu hamayya

platini
Image caption Michel Platini

An sake zaben shugaban hukumar kwallon Turai-Uefa Michel Platini a karo na biyu ba tare da hammaya ba.

Platini wanda zai kara wa'adin karin shekaru hudu akan kujerar, ya sha alwashin cigaba da tabbatar da ka'ida wajen yadda kulob kulob suke kashe kudadensu da yaki da zamba wajen wasa da kuma tashin hankali.

Tsohon kaptin din Faransa a jawabin shi ya dauki alkawarin bada fifiko wajen bukansa kwallon kasashe ta yadda gasar zakarun Turai za ta zama a bude, har yakai ga kananan kasashe zasu iya taka rawar gani.

Dan kasar Faransan, wanda ke jagorantar Uefa tun shekara ta 2007, an zabe shi ne a taron kolin Uefa, inda kowa a dakin taron ya mike tsaye don girmamashi.

Dan shekaru 55, Platini wanda a baya ya taka leda a kungiyoyin Nancy da St Etienne da Juventus ya kasance dan takara tilo daya nemi shugabancin na Uefa.

Shugaban Uefa din ya kuma jadadda bukatar cigaba da wanzar da dokar nan wacce zata tilastawa kulob kulob su dinga kashe kudadensu kamar yadda suke samu.