Adebayor da Keshi sun komawa Togo

togo
Image caption Tawagar 'The Hawks' ta Togo

Hukumar kwallon Togo ta samu kwarin gwiwa saboda labarin dawowar Stephen Keshi a matsayin Koci da kuma na dan wasanta Emmanuel Adebayor.

Dan kwallon Real Madrid Adebayor ya daina bugawa kasar kwallo ne bayan harin bindiga da aka kaiwa motar dake dauke da tawagar 'yan kwallon Togo lokacin gasar cin kofin Afrika a shekara ta 2010 inda aka kashe mutane biyu.

Adebayor ya tabbatarwa mahukunta kwallon kasar cewa zai buga wasansu na share fage a ranar Asabar tsakaninsu da Malawi.

Dan Najeriya Stephen Keshi a halin yanzu yana Togo don maye gurbin dan Faransa Thierry Froger.

Keshi a baya ya jagoranci Togo a shekara ta 2007 da kuma tsakanin 2004-2006,inda ya tsallakar da kasar zuwa gasar cin kofin duniya a 2006.