Euro 2012: Zamu kawowa Ingila cikas-Bale

bale Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Gareth Bale

Shaharren dan wasan Tottenham Gareth Bale ya ce yanada yakinin cewar Wales zata iya kawowa Ingila cikas a wasansu na neman gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Turai da za a buga a filin wasa na Millenium a ranar Asabar.

Wales a halin yanzu itace ta karshe a rukunin G, inda ta sha kashi a wasanninta uku na farko.

Amma Bale mai shekaru 21 ya ce tunda yanzu Gary Speed ne kocinsu, Wales za ta iya girgiza 'yan kwallon Fabio Capello.

Bale ya ce "bama jin tsoron komai, kuma muna da kwarin gwiwar cewa zamu taka rawar gani".

Gareth Bale ya haskaka matuka a tawagar Spurs, inda ya jikawa Inter Milan da AC Milan gari a gasar zakarun Turai.

Ganin cewar ya murmure daga raunin da yayi fama dashi na makwanni shida, Bale na saran taka irin rawar da yake yi a Spurs, cikin tawagar kasarshi Wales.