'Yan kwallon Liverpool uku zasu koma taka leda

gerrard
Image caption Steven Gerrard

Liverpool na saran 'yan kwallonta Steven Gerrard da Martin Kelly da Jonjo Shelvey zasu koma horo a mako mai zuwa.

Kaptin Gerrard ya yi jinya ta makwanni hudu, amma watakila ya buga wasansu da West Brom a gasar premier a ranar biyu ga watan Afrilu.

Mai horadda Liverpool Steve Clarke ya ce"sun murmure matuka, kuma Kelly da Gerrard zasu koma horo a mako mai zuwa".

Gerrard ya jimu ne a wasan da Liverpool ta casa Chelsea daci daya me ban haushi a Stamford Bridge a ranar shida ga watan Fabarairu.

Ciwon kafada ne kuma ya kwantar da Kelly da Aurelio a yayinda shi kuma Shelvey aka yi mashi tiyata a watan Fabarairu.

Labarin dawowarsu zai kara karfin tawagar Liverpool a yayinda suke shirin fafatawa da Manchester City a Anfeild a ranar 11 ga watan Afrilu sai kuma wasansu da Arsenal a ranar 17 ga watan Afrilu.