FA ta janye katin da aka baiwa Mensah

mensah
Image caption John Mensah

Sunderland ta samu nasara a daukaka karar data yi akan korar dan kwallonta John Mensah a wasan da suka sha kashi wajen Liverpool daci biyu da nema a ranar Lahadi.

An baiwa dan Ghanan jan kati nan take, wanda ke nufin an dakatar dashi na wasa guda,bayan sun yi taho mu gama da dan wasan Liverpool Luis Suarez.

Mensah bisa wannan hukuncin ba zai buga wasansu da Manchester City ba a ranar uku ga watan Afrilu.

Amma a yanzu zai buga saboda kwamitin da'a na hukumar kwallon Ingila ta janye dakatarwa da aka yi mashi.

Kocin Sunderland Steve Bruce yace:"mun godewa hukumar kwallo saboda amincewa da daukaka karar da muka yi,kuma muna murna John zai buga wasanmu da Manchester City".