Najeriya za ta fafata da Argentina a Abuja

nigeria
Image caption Kwallon da Heinz yaci Najeriya a Afrika ta Kudu

Najeriya za ta hadu da Argentina a wasan sada zumunci a ranar daya ga watan Yuni.

Za a buga wasanne a babban filin wasa na Abuja.

Kasashen biyu sun kara a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu a bara, inda Argentina ta samu galaba daci daya me ban haushi.

Shugban hukumar kwallon Najeriya NFF Aminu Maigari ya ce"babban labari ne za a buga wannan babban wasan a Najeriya".

Ya kara da cewar"'yan wasa da magoya baya da manema labarai sun jiran wannan ranar, inda babbar kasa a fagen tamaular duniya zata shigo kasarmu".

Najeriya za ta amfani da wasan don shiryawa fafatawar da zata yi da Ethiopia na neman gurbin zuwan gasar cin kofin kasashen Afrika a badi.

Argentina ta lashe gasar cin kofin duniya sau biyu wato a shekarar 1978 da kuma 1986.