Fifa zata hukunta Najeriya idan Moses ya buga

moses Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Victor Moses

Akwai yiwuyar a ragewa Najeriya maki a kokarinta na neman gurbin zuwa gasar cin kofin Afrika idan har ta saka Victor Moses ya buga mata kwallo ba tare da izinin Fifa ba.

Moses ya takawa Ingila leda a matakin 'yan kasada shekaru 21, amma a Najeriya aka haifeshi kuma a halin yanzu yana Abuja don shiga wasan Najeriya da Ethiopia da za a buga ranar Lahadi.

A ranar Laraba hukumar kwallon kafa ta duniya-Fifa ta bayyana cewar ba a mika mata takardar neman izini don dan wasan Wigan ya buga wasan.

Duk kasar data saka dan kwallon da bai kamata ba, za a rage mata maki sannan aci tarar ta.

Itama hukumar kwallon Ingila wato FA wacce ya kamata a tuntubeta, ta tabbatar da cewa babu wanda ya neme ta.

Sai dai ita kuma hukumar kwallon Najeriya NFF ta ce ta aike wa Fifa takardar neman izini a farkon wannan makon.

An haifi Moses ne a Kaduna, amma ya koma Ingila tun yana dan shekara 11, a yayinda ya bugawa Ingila kwallo a matakin 'yan kasada shekaru 17 da 19 da kuma 21.

Moses nada damar bugawa Najeriya ko Ingila, amma dole saiya nemi izinin Fifa.

Fifa ta tabbatar da cewar duk kasar data saka dan kwallon da bai kamata ba, za a rage mata maki, sannan ta biya akalla tarar Euro 6,500.