Ba a hannin mu Bale ya yi rauni ba-Redknapp

Bale
Image caption Gareth Bale yana haskaka wa bana a Tottenham

Kocin Tottenham Harry Redknapp, ya musanta kalaman da ke cewa Gareth Bale ya samu rauni tun kafin ya tafi domin bugawa kasarshi wasa.

Tun tuni dai aka cire Bale daga jerion 'yan wasan da za su taka wa Wales leda a karawar da za ta yi da Ingila a wasan share fage na gasar Euro ta 2012.

Kocin Wales Gary Speed ya ce dan wasan mai shekaru 21 ya samu rauni ne a lokacin da ya ke buga wa Tottenham.

Sai dai Redknapp ya shaida wa BBC 5 live cewa: "Ya kammala mintina 90 a wasan West Ham ranar Asabar, ba tare da wata matsala."