Sebastian Vettel ya lashe Australian Grand Prix

Sebastian Vettel Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sebastian Vettel ne na kokarin kare kanbunsa ne

Dan wasan da ke tuka motar Red Bull Sebastian Vettel, ya fara gasar Fomula 1 ta bana da kafar dama, bayan da ya lashe gasar Australian Grand Prix.

Lewis Hamilton ne ya zo na biyu sai dai takwaransa na McLaren Jenson Button ya kare ne a mataki na shida.

Dan kasar Rasha Vitaly Petrov na kamfanin Renault ya taka rawa sosai, inda ya kare a mataki na uku.

Yayin da dan kasar Scotland Paul di Resta ya zo na goma a wasansa na farko da ya taka.

Fernando Alonso na Ferrari ya doke Mark Webber na Red Bull domin kasancewa a mataki na hudu.