Capello ya ajiye manyan 'yan wasanshi

Capello
Image caption Fabio Capello ya dade yana kokarin bunkasa tawagar Ingila

Kocin Ingila Fabio Capello ya ajiye manyan 'yan wasanshi biyar a karawar da kasar za ta yi da Ghana a ranar Talata a wasan sada zumunta.

Kocin ya umarci kyaftin John Terry da Ashley Cole da Michael Dawson da Frank Lampard da kuma Wayne Rooney da su koma kulob dinsu.

Duka 'yan wasan biyar dai an fara wasan da Ingila ta doke Wales da ci 2-0 ranar Asabar da su.

Kocin na Ingila ya ce zai sauya baki dayan 'yan wasa sha dayan da zai fara wasa da su a ranar Talata.

Baya ga 'yan wasan uku, Kyle Walker ya koma Aston Villa sakamakon raunin da yake fama da shi.

Wannan matakin na nufin kocin zai sake nada wani sabon kyaftin a wasan na Ghana, bayan da Terry ya yi wasan farko a matsayin sabon kyaftin din kasar.