ACN: Afrika ta Kudu ta doke Masar

Afrika ta Kudu
Image caption Afrika ta Kudu na kokarin farfadowa a fagen kwallon kafa ta Afrika

Afrika ta Kudu ta doke Masar da ci 1-0, a ci gaba da fafatawar da ake yi domin neman shiga gasar cin kofin kasashen Afrika ta 2012.

Itama Senegal ta doke Kamaru da ci daya mai ban haushi, yayin da Burkina Faso ta lallasa Namibia da ci 4-0.

Sai Kenya da ta doke Angola da ci biyu da daya a karawar da suka yi a birnin Nairobi.

Sakamakon wasu daga cikin wasannin da aka buga

Malawi 1 - 0 Togo Tanzania 2 - 1 Central African Republic Rwanda 3 - 1 Burundi Chad 0 - 1 Botswana Guinea Bissau 0 - 1 Uganda Cape Verde 4 - 2 Liberia Senegal 1 - 0 Cameroon South Africa 1 - 0 Egypt Burkina Faso 4- 0 Namibia Mali 1 - 0 Zimbabwe