An ci tarar Birmingham City fam 40,000

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kungiyar Birmingham bayan sun lashe gasar kofin Carling

Hukumar kwallon Ingila ta ci tarar Birmingham City fam dubu 40,000 bayan magoyan bayan kungiyar sun shiga filin wasa a wasa dab da kusa dana karshe da kungiyar ta buga da Aston Villa.

Sama da magoya bayan kungiyar dubu daya su ka shiga filin wasa a wasan da kungiyar ta yi nasara akan Aston Villa da ci biyu da guda.

Harwa yau Hukumar ta ja kunnen kungiyar da kada suka kara bari irin hakan na ya faru nan gaba.

An dai samu dan rikici tsakanin magoya bayan kungiyoyin biyu a lokacin da magoya bayan Birmingham su ka shiga filin wasa.